Yadda Al'ummar India Ke Alhinin Mutuwar Gawurtacciyar Damisa Mai 'ya'ya 29 - Bbc Information Hausa

Daga SharanyaHrishikeshBBC News, Delhi

18 Janairu 2022Asalin hoton, Varun ThakkarBayanan hoto,

Collarwali ba ta bbc hausa news arsenal da wasa wurin farauta amma kuma an san ta da haba-habaGawurtacciyar damisar India ba damisa ba ce karabiti, kamar kowace damisa.Daya daga cikin damisar da ta yi fice a kasar mai suna Collarwali ta rasu a karshen mako tana da shekara sixteen. Ta taka muhimmmiyar rawa wajen raya gandun dajin da ta yi rayuwarta, wato Gandun Dajin Damisa na Pench, wanda ke jihar Madhya Pradesh.An sanya mata suna (Collarwali) saboda kwalar sadarwa da aka sanya mata a wuya, inda ta haifi 'ya'ya 29 a haihuwa takwas tsawon rayuwarta ta shekara 16, wanda wannan babban abin tunawa ne, in ji wani ƙwararre.Ta zama ɗaya daga cikin fitattun damisa da aka sani a India bayan da aka sa ta a fim ɗin namun daji na BBC, Spy inside the Jungle, wanda a cikinsa aka riƙa bin diddigin rayuwar 'ya'yan damisa hudu tsawon shekara biyu.Fim din ya ja mutane 'yan yawon bude idanu suka riƙa tururuwa zuwa gandun dajin, inda yawancinsu suka riƙa tambayar inda wannan damisa Collarwali da mahaifiyarta mai kwarjini take, in ji Prabir Patil, mai rajin kare dabbobi wanda ya fara mu'amula da gandun Pench a 2004.A ranar Asabar da yamma Collarwali ta rasu sakamakon rashin lafiyar da ke da alaƙa da tsufa.Asalin hoton, Aniruddha MajumderBayanan hoto,

An sanya wa Collarwali na'urar sadarwa a wuyanta a 2008Masu rajin kare dabbobi da jami'an gandun daji da kuma masu daukar hoto na namun dawa sukan yawaita yin magana a kan wata dabba da ta girma a gabansu a gandun.Gandun da suka yi amanna shi ne ya ja hankalin Rudyard Kipling ya rubuta littafinsa na gandun daji, The Jungle Book.An haife ta ne a 2005 da laƙabin T-15 - haka ita ma mahaifiyarta wadda ake kira "badi mata" ko "babbar uwa" damisa ce da ta yi fice. Sunan mahaifinta T-1. Daga baya ana kiranta da suna Collarwali - wato mai kwala - lokacin da ta zama damisa ta farko a dajin da aka sanya mata kwala da ke dauke da na'urar sadarwa a wuyanta, na'urar da ta bayar da damar sanin hali da kuma inda damusar take a tsawon shekaru.Haka kuma masu sha'awar namun daji na kiranta da suna "mataram"ko "uwa ta gari" sunan da suka sanya mata saboda irin halayyarta da mutane suka sani tsawon lokacin rayuwarta. Asalin hoton, Varun ThakkarBayanan hoto,

Collarwali sananniya ce a gandun daji na PenchMista Patil ya ce, "kafin a haifi Collarwali ba kasafai ke ganin damisa ba a gandun daji na Pench. To amma nan da nan sai ya kasance ita aka fi gani a nan. Mai rajin kare dabbobi Vivek Menonna kiranta ''fuskar Pench'' ("face of Pench"), yana mai nuni da irin halayyarta ta daban, abin da ke sa yawancin masu ziyara da masu daukar hoto su mayar da hankali a kanta da kuma 'ya'yanta.Ba kasafai Collarwali take saba wa da masu ziyara a Pench ba, in ji Mohammed Rafique Sheikh, mai rajin kare dabbobi wanda ya girma a yankin gandun dajin.Mista Sheik wanda ya jagoranci daruruwan masu ziyara shiga gandun ya ce, "dabba ce mai son mutane wadda za ka ga ta zo kusa da motar masu yawon buɗe idanu ba tare da wani tsoro ba."Sama da kashi 70 cikin dari na damisar da ke duniya na India. Yawansu na raguwa a da amma kuma yanzu sun karu zuwa 2,976 kamar yadda kiyasin gwamnati na baya-bayan nan ya nuna.Kowa ce shekara dubban masu yawon bude idanu na tururuwa zuwa gandun damisa fifty one da ke warwatse a fadin India da zummar ganin wannan damisa mai kwarjini da kasaita.Collarwali ta fita daban ta hanyoyi da dama, bayan da ta kafa yankinta na kanta"a kusa da mahaifiyarta".Ba kasafai take barin wannan yankin ba, kuma a iya nan ta tsaya duk tsawon rayuwarta har ta mutu."Tana da girma sosai ta yadda sauran damisa ke tsoron fada da ita. Wani lokacin ma jami'an dajin da ke kula da wasu wuraren na daban inda damisa take suna daukar cewa namijin damisa ne idan suka ganta saboda girmanta.A lokacin akwai 'ya'yan dmisa 29, inda 25 daga cikinsu suka rayu - abin da ba a taba samu ba a India kila ma da duniya baki daya.'Ya'yanta uku na farko sun mutu ne a sanadiyyar cutar sanyin haƙarƙari wato nimoniya (pneumonia) a 2008.To amma nan da nan ta faranta wa ƙwararru rai inda ta riƙa haihuwa bayan haihuwa a dan tsakankanin lokaci, inda har ma ta haifi biyar a lokaci daya a 2010, wanda abu ne da ba kasafai ake iya gani ba, in ji ƙwararru.Asalin hoton, Varun ThakkarBayanan hoto,

Collarwali ta haifi 'ya'ya 29 a tsawon rayuwartaYayin da galibin damisa ke zama da 'ya'yansu ba sa yaye su tsawon sama da shekara biyu, Collarwali tana ƙoƙarin ganin nata ƴaƴan sun zama masu dogaro da kai tun kafin wannan lokaci, ta hanyar barinsu su kaɗai a wuraren da ake da tarin dabbobin da za su iya kamawa su ci.Uwa ce mai ƙarfi da ƙoƙarin gaske, inda a wani lokacin take kashe nama biyu a rana domin ciyar da 'ya'yanta, in ji Dr Akhilesh arsenal Mishra, likitan da ke kula da dabbobin wannan gandun daji, wanda sau da dama ya yi wa Collarwali magani a lokacin rayuwarta.Yana daukar kansa a matsayin daya daga cikin mutanen da suka yi sa'a a duniya saboda samun damar yin aiki a kan wannan damisa.Mai fafutukar kare dabbobi kamar Mr Menon ya yaba da Collarwali kan yadda ta sa gandun dajin Pench ya zama wata matattara mai tarin damisa, a lokacin da take ganiyar lafiyarta kenan. Ya ce wannan na daga cikin abubuwan da ta bari na tarihi, tare kuma da yawan 'ya'yan da ta haifa.Jikokinta suma solar bi layi inda suke ta hayayyafa ake samun karuwar yawan damisa a gandun.Duk wanda BBC ta yi magana da shi za ka ji yana da wani labari mai dadi da ya sani a sport da Collarwali - Mr Patil yana iya tuna lokacin da ya ga damisar da wasu 'ya'yanta uku lokacin da suka far ma wata damisamai rodi-rodi da ke jin yunwa, suka bi ta har saman bishiya lokacin da ta shigo yankinsu tana farauta.Shi kuwa mai daukar hoton namun daji Varun Thakkar, yana iya tuna yadda ya ganta ne tare da wasu fitattun 'ya'yanta biyar sun baje suna shan iska a shekara ta 2011- Su su shida suna hutuwa a kan wani dutse a kusa da gabar kogin gandun dajin na PenchBayan shekara goma sha daya har yanzu bai manta da wannan yanayi da ya ganta da 'ya'yan nata biyar ba.Dr Mishra ya ce wannan damisa mai basira yawanci za a ka ga ta kwanta a fili idan ba ta da lafiya ko kuma an ji mata rauni, kai ka ce tana jiran taimako ne daga mutane, wadanda su ke kula da ita.Asalin hoton, Pench ReserveBayanan hoto,

An kona gawar Collarwali bayan da mutane suka yi mata ban-kwanaHaka ta yi ana sauran kwana daya ta rasu ma, a lokacin ta galabaita ba ma ta iya tafiya sosai, kamar yadda wani da y ganta ya fada.An kona gawar Collarwali a ranar Lahadi a wani fili a cikin gandun dajin bayan da ma'aikatan wurin da masu kare dabbobi da kauyawan yankin solar yi addu'o'i da ajiye mata furanni.Wani hoton bidiyo da ma'aikatan gandun suka yi na jana'izarta, yana farawa da hotonta hana zaune a ciyawam cikin kwanciyar hankali a garkenta, yayin da kalmar sunanta Collarwali ke bayyana a talabijin.Yadda mutanen da suka santa za su tuna da ita kenan.Duk da irin rashin da aka yi na Collarwali wadda kusan damisa ce da za a ce babu wata kamarta, Dr Mishra ya ce ba sa alhini ko makokinta, maimakon haka suna su su yi bikin tunawa da abubuwan da ta bari na tarihi."Ta yi cikakkiyar rayuwa ta farin ciki," In ji Mista Sheik. "Mutuwarta ta girgiza mu, amma za ta ci gaba da kasancewa tare da mu a zuciyarmu."

Komentar